Putin: Huladar Gas da Jamus ba fashi
May 18, 2018An yi ta kai ruwa rana tsakanin gwamnatocin Mosko da Berlin tun lokacin da Rasha ta mamaye yankin Kirimiya shekaru hudu da suka wuce, amma suna da muradu iri daya a dangane da aikin shimfida batutun gas da ake wa lakabi da Nordstream 2 wanda zai ba wa Rasha damar tura karin iskar gas zuwa arewacin Turai.
A wannan makon an jiyo wani jami'in gwamnatin Amirka na cewa Washington na da damuwa game da shirin, sannan kamfanonin da ke cikin aikin shimfida batututun Gas din na Rasha suna cikin babbar barazanar fuskantar takunkuman Amirka.
Ita ma a nata bangaren shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta jaddada muhimmancin aikin musamman a fannin tattalin arziki duk da matsalolin da ke akwai.
Yayin ziyarar Merkel a Rasha, Putin ya bukaci hadin kan sauran kasashen Turai da kungiyoyin agaji wajen sake gina kasar Rasha da yakin basasa ya lalata. Putin ya gana da shugaban Siriya Bashar al-Assad kwana guda gabannin ganawarsa da Merkel.