1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin Gaza abin kunya ne - Qatar

Abdul-raheem Hassan
December 5, 2023

Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani ya ce "ci gaba da lugugen wuta da ake yi a Gaza, abin kunya ne ga kasashen duniya masu fada a ji" kasar ta ce ana kan tattaunawa don lalubo bakin zaren warware rikicin.

https://p.dw.com/p/4ZoPU
Sarkin Qatar, Tamim bin Hamad Al ThaniHoto: Vyacheslav Prokofyev/SNA/IMAGO

Sheikh Al-Thani ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya tilasta wa Isra'ila komawa kan teburin tattaunawa don kawo karshen zubar da jinin fararen hula a Gaza. Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Firaiministan kasar Sheikh Mohammed Bin Abdulrahman al-Thani ya ce ana kan tattaunawa da zimmar kawo karshen yaki tsakanin Hamas da Isra'ila.

Hukumomin lafiya karkashin jagorancin Hamas a Gaza sun ce yakin ya kashe mutane sama da 15,800 a yankin Falasdinu kadai, tun bayan fara yakin a ranar bakwai ga watan Oktoban 2023.

Qatar ta taimaka wajen shiga tsakani bangarorin da ke gaba da juna wadda ta ba da damar sako 'yan Isra'ila da dama da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su, da kuma sakin fursunonin Falasdinawa sama da 200.