1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Sabuwar sigar DW: Abin da ya sa muka bambanta

December 11, 2023

DW ta samu sabuwar siga, wadda ke mayar da hankali kan saukaka amfani da kafar intanet dinta. Babbar Edita Manuela Kasper-Claridge ta bayyana wasu muhimman sauye-sauye da masu binmu ta internet za su iya gani.

https://p.dw.com/p/4a2YU
Shafin internet da App na DW a cikin sabuwar siga
Shafin internet da App na DW a cikin sabuwar sigaHoto: DW

Wani sabon salo, kyakkyawa kuma ingantacciyar siga ga masu amfani - wannan shi ne abin da jami'an fasalta kafar internet dinmu suka yi ta aiki a kai tsawon watanni. Ina so in nuna muku wasu daga cikin sababbin abubuwa da muka bijiro da su.

Haduwa da samun dama sune jigon kirkirar sabon tsarin na ma'aikatarmu. A nan gaba, da yawa daga cikin abubuwan da muke gabatarwa za su kasance marasa shamaki.

An inganta shafinmu na internet da manhaja (app) don saukaka bibiyarmu ta internet.

Godiya ga ingantaccen shafin internet, za ku sami bayanan da kuke bukata cikin sauri. Muna sauya sigar rubutunmu don saukaka muku karatu. Sauye-sauye na zahiri a "menus" da na bayan fage suna tabbatar da bayyanarmu da karfafa gane mu a matsayin ingantaccen tushen bayanai.

Launuka hade da bayanai suna samun sabuntawa mai inganci. Kuna iya sa ido don ganin karin launuka da zane-zane masu ban sha'awa wadanda ke saukaka fahimtar bayanai.

Muna son abubuwan da muke yi su samu cikin sauri da kuma saukin ganewa. Muna son ku ji dadin amfani da shafunkanmu na internet da kuma app.

Kuma yanzu sabuwar siga a dw.com ta fara. A cikin watanni masu zuwa, karin sauye-sauye za su biyo baya a duk dandamali da za ku iya samun labaran DW.

Da fatan za ku bayyana mana ra'ayoyinku da kuma abubuwan da kuka gani game da sabuwar sigar ta DW. Muna jiran ra'ayoyin ku.