Ra'ayin gwamnatin Najeriya bayan hare-hare a jihar Kano
January 22, 2012Murtanin da shugaban Najeriyar Goodluch Jonathan ya yi da ke kusnhe a sanarwar da ya bayar da ta zo fiye da saoi 24 da afkuwar wannan mummunan lamari da ya afkawa jihar Kanon wanda ya zama harin da yafi kowanne muni tun da Najeriya ta afka cikin wannan mummunan hali.
Shugaba Goodluck Jonathan ya mika ta'aziyarsa ga yan uwan mutanen da suka mutu a dalilin harin. Na tambayi Dr Reuben Abati mai baiwa shugaban Najeriyar shawara a fannin yada labaru ko wane mataki gwamnatin ke shirin dauka a kan wannan lamari ?
Yace gwamnati ta yi alkawarin ci gaba da fatattakar dukannin masu aikata ta'adanci, kuma tun kafin wannan lokaci jamia'an tsaro sun kasance cikin damara ta shirin ko ta kwana domin fsukantar wannan sabon kalubalen da muke fuskanta.
Tuni dai ake ta maida murtnai tare da da kira ga gwamnatin ta dauki matakai na sadidan don shawo kan matsalar da suka hada da sulhu, Sanata Kabiru Gaya da ya fito daga jihar Kano ya bayyana matakan da yake gani ya kamata a dauka.
To ko gwamnatin na tunanen bin hanyar lalama don sulhuntawa da yayan kungiyar Ahli Sunnah li da'awati wal jihad da suka sanar da daukan nauyin kai harin ? Hari la yau ga Dr Reuben Abati
Yace nasan inda tambayarka ta nufa kana son ka ce ko gwamnati zata sulhunta da yan Boko Haram, to na yi maka bayani, gwamnati ta kuduri aniyar bin dokokin kasa sau kafa tare da kare rayuka da dukiyoyin jama'a, wanda shine zahirin aikin da ke kan gwamnati.
A yayainda ake ci gaba da aikin kai dauki ga wadanda suka jikkata har yanzu babu bayani na hukuma a kan addain mutanen da suka rasu, sai dai majiyoyin da ba na gwamnati ba na cewa mutanen da suka mutu sun zarta 200. Na tambayi Malam Musa Ilalah jami'in kula da shiyyar arewa maso yammacin Najeriya na hukumar kai daukin gaggawa don jin halin da ake ci a yanzu.
A yanzu dai yan Najeriya sun zura idanu su ga matakin da gwamnati zata dauka don maido da zaman lafiya da yankin arewacin najeriyar ke tinkaho da shi, wanda subucewarsa ke jefa kasar cikin mawuyacin hali da ya sa yanayin tsaron kasar ci gaba da tabarbarewar gwamma jiya da yau. Bomb
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Umaru Aliyu