Rabuwar kanu cikin jam´iyar adawa ta UFC a Togo
May 29, 2010Talla
A birnin Lome na ƙasar Togo dubun dubatar jama´a ne, suka shirya zanga-zangar lumana, domin nuna goyan baya ga matakin da shugaba Faure Yasimbe ya ɗauka na girka gwamnatin haɗin kan ƙasa, wadda ta ƙunshi babbar jam´iyar adawa ta UFC.
Dalili da girka wannan gwamnati an samu rabuwar kanu a jam´iyar ta UFC.Wani gungun membobi a komitin ƙoli ya yanke shawarar tsige shugaban jam´iyar Gilchrist Olympio wanda ya rattabawa yarjejeniyar hannu ranar Laraba da ta wuce.
Jean Pierre Fabre ɗan takara jam´iyar UFC a zaɓen shugaban ƙasar Togo da ya wakana a watan Maris na wannan shekara ya ce Gilchrist Olympio, ya yanke wannan shawara ba tare da sanin uwar jam´iya ba.
Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohamed Nasiru Awal