1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoni: Cire takunkumi zai warware rikici

Abdoulaye Mamane Amadou
December 9, 2020

Iran ta ce a shirye take da ta mutunta yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da kasashen duniya matikar suka sakar mata mara kan takunkuman da suka kakaba mata na karayar tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/3mUrM
 Hassan Rouhani Präsident Iran
Hoto: Alexei Druzhinin/Sputnik/AFP

A wani jawabinsa da aka yada a gidan talabijin din kasar Iran a wannan Laraba, Shugaba Hassan Rohani ya ce duk lokacin da manyan kasashen yamma suka dawo kan mutunta alkawuran da suka daukar wa Iran, kasar a shirye take da ta girmama duk wasu alkawuran da ta dauka na dakatar da bunkasa ayyukanta na makamashin nukliya.

Tun bayan da Amirka ta janye jiki daga yarjejeniyar a shekarar 2018 tare da lafta wasu karin takunkuman karayar tattalin arziki, Iran ta rungumi matakin tuntubar wasu kasashe na nahiyar Turai da su juya wa matakin Amirka baya domin ci gaba da mutunta yarjejeniyar Vienne ta 2015.