1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoto a game da halin 'yan gudun hijira a Jamus

September 29, 2017

Kungiyar agaji ta cocin Katolika watau Malteser ta fitar da sabon rahoto kan halin 'yan gudun hijira a nan Jamus.

https://p.dw.com/p/2kxIp
Indonesien, Präsident Joko Widodo in Flüchtlingscamp auf Bali
Hoto: Laily Rachev/Biro Pers Setpres

Rahoton wanda ke da burin matsa kaimi kan majalisar dokoki ta dauki mataki ya nuna cewar sabbin 'yan gudun hijira da suka shigo kasar ta Jamus na fuskantar matsaloli. A baya dai gwamnatin tarayya ta gabatar da rahotanni har guda goma sha daya game da sajewar baki a Jamus. Na baya-bayan nan shi ne kan yawan kwararar 'yan gudun hijira da suka shigo kasar. A yanzu kuma kungiyar agaji ta Malteser ta cocin Katolika ta gabatar da na ta rahoton. Rahoton mai shafi 112, ya yi cikakken bincike tare da nazari ta fannin kimiyya kan batun 'yan gudun hijirar, Ita dai  kungiyar agajin ta Malteser ta dade tana da masaniya game da rayuwar 'yan gudun hijira bisa tallafa musu da ta ke yi. Shugaban kungiyar ta Malteser a nan Jamus Karl Prinz zu Löwenstein, ya ce manufar rahoton ita ce samar da yanayi na muhawara kan batun na 'yan gudun hijira. Prinz zu Löwenstein ya ce sun zabi wallafa rahoton ne bayan zaben majalisun dokokin Jamus domin gabatar da binciken  ga sabuwar majalisar, ta yi muhawara da kuma nazari a kansa. Lars Peter Feld  daraktan cibiyar nazarin tattalin arziki ta Freiburg wadda ta gudanar da bincike ta fuskar nazarin kimiyya kan batun na 'yan gudun hijira, ya ce tun karshen yakin duniya na biyu, batun samun aiki ga 'yan cirani da 'yan gudun hijra batu ne da a ko da yaushe yake tasowa idan aka yi maganar sajewar baki cikin al'amuran kasa.