Rahoton hukumar samar da makamashin Nukliya ta duniya akan Iran
November 9, 2011Hukumar samar da makamashi nukliya ta duniya ta baiyana fargaban ta dangane da shirin ƙasar Iran na nukliya wanda ta zargi ƙasar da yunƙurin ƙera makamin ƙare dangin,a cikin wani rahoton da hukumar ta baiyana ta ambato cewar ƙasar ta Iran ta ƙera wani makamin Atom da ka iya zama babbar barazana ga zaman lafiya a duniya.
Sai dai a halin da ake ciki ƙasar ta Iran na ci gaba da dagewa akan masayin ta na mallakar nukliyar domin amfanin fara fula,a cikin wani jawabi da ya yi shugaban ƙasar na Iran ya ce barazanar da Amurka da kuma Isara'ila ke yi wa ƙasar sa ba wani sabon abu ne kuma ya musunta zargin.Kuma gwamnatin ƙasar ta yi shelar ci-gaba da aiwatar da shirin du da rahoton da ta baiyana ,nan gaba ne hukumar za ta baiyana rahoton a hukumce.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman