Rahoton shekara na UNDP kan Afirka
May 15, 2012Hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya, wato UNDP, ranar Talata a birnin Nairobi, ta gabatar da rahoton ta na shekara, a game da ci gaban jama'a a nahiyar Afirka, da kuma dangantakar dake akwai tsakanin matsayin rayuwa da kokarin nahiyar take yi na tabbatar da isasshen abinci ga dukkanin al'ummar wannan yanki. Hukumar ta UNDP tace nahiyar Afirka ba zata sami nasarar ci gaba da kiyaye bunkasar tattalin arzikin da take samu a yanzu ba, saiidan an kawar da matsalar yunwa dake addabar akalla kashi daya cikin kashi hudu na mazauna nahiyar.
A rahoton da hukumar ta UNDP ta sanya masa suna kokarin tabbatar da isasshen abinci a Afirka, ta baiyana bakin cikin ganin cewar bunkasar tattalin arziki da ake samu yanzu a yanzu, bai taimaka ga samun karuwar abinci tsakanin masu bukata ba. Kakakin hukumar UNDP, Helen Clark wadda ita ce ta gabatarda rahoton na shekara a birnin Nairobi, tace maida hankali kan bbatun noma kadai ba zai warware matsalar karancin abinci a Afirka ba. Ana bukatar kyautata matakan jin dadin zaman jama'a a yankunan karkara da kyautata hynyoyin kiwon lafiya da baiwa kananan manoma damar mallakar gonaki da taimakon kansu da kansu.
Hukumar UNDP tace abin bakin ciki ne ganin cewar ko da shike akwai rarar abinci mai yawa a duniya baki daya, amma yunwa da rashin isasshen abinci kai gina jiki har yanzu suna addabar mazauna mnahiyar Afrika, musmaman na kudu da hamadar Sahara a yankin Sahel. Kazalika, duk da bunkasar tattalin arziki da nahiyar Afrika take samu, amma hakan bai yi jagora ga kyautata bada ilimi ba ko kyautata jin dadin zaman jama'a da bunkasa samar da abinci.
Nahiyar Afirka, inji rahoton, shine yankin da yafi fuskantar matsalar karancin abinci a duiya baki daya, inda akalla kashi daya cikin kashi hudu na mazauna yankin miliyan 856 suke fama da yunwa ko karancin abinci mai amfani a jiki. A yanzu haka, mutane fiye da miliyan goma sha biyar ne suke fuskantar yiwuwar rasa rayukan su saboda yunwa a yankin Sahel abin da ya hade kasashen Senegal, Chadi, da jamhuriyar Niger, har ya zuwa yankin kahon Afirka, kamar Djibuti da Habasha da Kenya ko Somalia.
Helen Clark, ta hukumar UNDP, wadda ita ce ta gabatar da rahoton ranar Talata, tace tabbatar da isasshen abinci, kamar yadda aka shimfida lokacin taron kolin abinci na duniya a shekarata 1996, yana nufin ko wane dan Afirka ya kasance da damar samun isasshen abinci kuma mai gina jiki a duk lokacin da yake da bukata, domin tabbatar da rayuwa da koshin lafiyar sa. Tace ana iya samun nasarar tabbatar da isasshen abincin ga kowa da kowa a Afirka idan aka kiyaye wasu sharudda da suka hada har da kara bunkasa noma da kawo karshen rikon sakainar kashi da ake yiwa noman, tare da goyon bayan mata manoma, wadanda sune masu samar da mafi yawan abincin da ake nomawa a Afirka, sai kuma baiwa kananan yan kasuwa da masu sarrafa kayan amfanin gona kwarin gwiwa.
Rahoton ya ambaci kasashe kamar Ghana da Malawi, wadanda yace sun sami ci gaba matuka a kokarin su na cimma burin Millenium nan da shekara ta 2015, a fannin samarwa jama'ar su isasshen abinci.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar