CENI ta sanya ranar yi wa 'yan Nijar rajista a ketare
September 1, 2022Ganawar ta yini daya wace Hukumar Zaben kasar ta Nijar ta shirya, ya samu halartar wakillan bangarorin jam'iyyun kasar tun daga bangaren masu mulki zuwa na 'yan adawa da ma 'yan ba ruwanmu. Hukumar ta CENI ta bayyana masu jadawalin soma aikin rijistar masu zaben a ketare da kuma tattaunawa kan sauran batutuwan da suka shafi aikin gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar ta Nijar a kasashen ketare.
''A kasashe 15 ne za mu yi wannan aiki. Cikinsu akwai kasashen Afirka da Turai da Amirka. A ranar 15 ga watan Oktoba za mu fara rajistar.'' in ji Dr Aladoua Amada, mataimakin shugaban hukumar zaben kasar ta Nijar.
Kwanaki 14 za a kwashe ana gudanar da aikin rajistar zaben a katare. Kuma duk wani dan Nijar da ke da takardar haihuwa ta kasar na da damar yankan katin na zabe. Sai dai wasu jam'iyyun kasar ta Nijar na ganin akwai bukatar kawo gyara a cikin tafiyar.
Ousmane Sidien shugaban jam'iyyar APC a 'Zauna Tare' ya shaida wa DW cewa ''CENI ta yi mana katin zabe mara inganci a nan Nijar. Ya kamata hukumar ta zamanantar da katin zaben da take bayarwa.''
Duk da wannan dai tuni wasu jam'iyyun kasar ta Nijar suka sanar da soma aikawa da wakilansu a kasashen ketaren domin fadakar da magoyan bayansu a game da bukatar ba da hadin kai ga aikin rijistar masu zaben.
Hukumar zaben kasar ta kiyasta cewa aikin rijistar ‘yan Nijar mazauna ketaren zai shafi mutum kimanin 180,000 da ke rayuwa a wajen kasar.