Rakka - 'Yan IS sun rasa babbar maboyarsu
Sojojin Siriya da mayakan Kurdawa sun yi nasarar fatattakar 'yan IS daga Rakka ba tare da babbar turjiya ba.
Shataletalen Azaba a Rakka
Babban filin wasa na birnin na Arewacin Siriya nan ne tunga ta karshe ta IS. Wani da ya ganewa idanunsa ya ce sojojin SDF na Siriya sun kafa tutarsu a wurin a ranar Talata. A cewar rundunar sojin ta SDF yaki ya kare a Rakka. 'Yan tsirarun mayakan IS suka rage wadanda ke nuna turjiya.
A kan hanya zuwa Rakka
Sojojin Siriya suna jinjinar nasara yayin da suke kan hanyar shiga garin Rakka a ranar Litinin. Har yanzu mayakan da aka yiwa kawanya sun ja daga a tsohuwar daular su. Dakarun sojin Siriya SDF ta kunshi galibi mayakan Kurdawa da na Larabawa.
Mamayar birnin da aka yi wa kaca-kaca
Tankokin yaki na kutsawa ta baraguzai a cikin garin da aka kwashe shekaru ana fafata yaki. A 2014 mayakan IS suka kwace garin inda suka mayar da shi daular su. Daga nan suke kitsa kai hare hare a kasashen duniya. A watan Nuwambar bara sojojin Siriya suka kaddamar da farmaki a kan Rakka.
Daga nesa: Hangen asibitin birnin
Wani gwanin harbi na sojojin SDF ya yi kwantar bauna daura da asibitin Rakka. Asibitin na daya daga cikin tunga ta karshe da mayakan IS suka ja daga kamar dandalin Naeem da ke tsakiyar birnin. Yankunan biyu sun kai sojojin har zuwa Litinin ana fafatawa inda aka kashe mayakan IS da dama.
Tutar nasara
Sojojin SDF sun kafa tutarsu a kan wani gini kusa da asibitin da aka gwabza yaki. Bayan bakar tutar IS, tuta mai launin rawaya da shudi mai haske na sojojin SDF sun mamaye birnin. Cikin kwanaki masu zuwa sojojin SDF na Siriya za su fara binciken nakiyoyi da aka binne a karkashin kasa da sauran sansanoni na 'yan tawayen
Hankali ya kwanta
Mayakan SDF na yi wa juna barka na kawo karshen yakin Rakka. A kusa da filin wasa da kuma asibiti, dandalin Naeem ya kasance wuri na karshe da ke karkashin ikon IS. "Shataletalen azaba" kamar yadda ake yiwa wurin lakabi shekaru uku da suka wuce, a nan IS ta rika aiwatar da kisa. Mutanen da aka kashe a bainar jama'a ana barin gawarwakinsu tsawon kwanaki.
Kaura daga birnin da ake barin wuta
Fararen hula 3000 sun sami damar ficewa daga garin karkashin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugabannin al'ummar yankin da mayakan Jihadi. Hakan na nufin kusan dukkan mazauna Rakka sun sami zuwa tudun mun tsira. Rahotanni daga Rakka na cewa har yanzu akwai ragowar mayakan IS yawanci na kasashen waje da suka zauna suke cigaba da turjiya.
Hanyar tsira
Bayan tsawon watanni ana gwagwarmaya a birnin wanda ya taba kasancewa da mutane fiye da dubu 200 a cikinsa, wadannan mutane na ficewa daga yankin. Sun bar birni da yaki ya yiwa kaca-kaca da alamun harbin bindiga a ko ina. Ba su da tabbas kan makomar su.