1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kawancen Saudiyya ya tsagaita wuta a rikicin Yemen

March 30, 2022

Sai dai tuni mayakan Houthi suka yi watsi da wannan tayi, inda suka ce babu wata tsagaita wuta mai ma'ana idan har kawancen na Saudiyya bai bude tashoshin jiragen ruwan kasar na Yemen ba.

https://p.dw.com/p/49D3i
Jemen | pro Regierungskämpfer in Schabwat-Provinz
Hoto: AFPTV/AFP/Getty Images

Kawancen kasashen da Saudiyya ke jagoranta a yakin da suke yi da mayakan Houthi na kasar Yemen ya sanar da cewa zai tsagaita. Matakin ya biyo bayan rokon da MDD ta yi cewa bangarori biyun su dakatar da barin wuta albarkacin zuwan azumin watan Ramadana. 

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kawancen Saudiyyar Turki al-Maliki ya fitar, ya ce za su yi duk mai yiwuwa wurin ganin tsagaita wutar da ake sa ran za ta fara aiki a ranar Asabar ta wannan mako ta yi nasara.

Tun daga shekara ta 2015 ne dai mayakan Houthi da Iran ke goya wa baya a rikicin Yemen ke musayar wuta da kawancen Saudiyya da ke samun goyon bayan hukumomin Riyadh, lamarin da ya tilasta wa dubban mutanen Yemen kaurace wa gidajensu.