1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rana ta biyu ta ziyarar Paparoma

November 28, 2017

Paparoma Francis ya gana da babban sojan kasar Myanmar, inda babban jami'in ya karyata zargin da duniya ke yi wa kasar na daukar mummunan mataki kan musulmi 'yan kabilar Rohingya.

https://p.dw.com/p/2oMvQ
Myanmar Papst Franziskus
Hoto: Reuters

Paparoma Francis wanda ke ziyara a kasashen Myanmar da Bangaladash, ya gana da babban sojan kasar Myanmar janar Min Aung Hlaing, inda babban jami'in ya karyata zargin da duniya ke yi wa kasar na daukar mummunan mataki kan musulmi 'yan kabilar Rohingya. Akalla dai musulmin marasa rinjaye dubu 620 suka tsallaka gabashin jihar Rakhine zuwa Bangaladash, saboda kisan gilla da sojin Myanmar suka yi masu.

Majalisar Dinkin Duniya da Amirka duk sun hada baki wajen bayyana lamarin a matsayin kokari ne na shafe al'umar ta musulmi daga doron kasa, sakamakon kashe-kashen da suka wakana cikin watan Agustan bana. Matakin da sojin na Myanmar kan mutanen ne dai makasudin ziyarar ta Paparoma a yankin, tare kuma da ganawa da wasu tsirarun 'yan darikar Katolika da ke a kasar.