1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

rangadin Merkel a gabas ta tsakiya

April 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuOQ

A ranar ƙarshe ta ragadin da ta kai a yankin gabas ta tsakiya, shugabar gwamnatin Jamus Angeller Merkel, ta bayyana gamsuwa a game da tantanawar da ta yi da shugabani daban-daban na wannan yanki, wanda batun zaman lahia ya rataya kan su.

Daya bayan ta gana da sarki Abdallah na Jordan, da Praministan Isra´ila, Ehud Olmert, da kuma shugaban hukumar Palestninawa Mahamud Abbas.

A yayin da ta ke bayani ga yan jarida, shugabar gwamnatin Jamus, ta ce dukan ɓangarorin, sun bayyana mata shawar kawo ƙarshen rikicin Isra´ila da Palestinu.

Sannan ta yi matuƙar yabo, ga saban yunƙurin shugabanin ƙasashen larabawa, mussamman bayan taron da su ka kira a birnin Ryad na Saudi Arabia a makon da ya gabata.

A yayin da ta gana da shugaban hukumar Palestinawa, Merkell ta nunar da cewa, ƙungiyar gamayya turai, a halin ba zata hau tebri guda ba da Hamas, wadda ta ɗauka a matsayin ƙungiyar ta´ada.