Rarrabuwar kawunan ƙasashen duniya game da Iran
January 21, 2012Manyan ƙasashen duniya sun bayyana aniyar farfaɗo da tattaunawa tsakaninsu da Iran game da shirinta na nukiliya. Sai dai kuma suna ci gaba da fuskantar rarrabuwar kawuna dangane da matakan da ya kamata a ɗauka domin ja ma shirinta na inganta Uranium birki. Wannan matakin na su ya zo ne makwanni ƙalilan bayan da taƙaddamar da aka fuskanta tsakaninsu bayan da Iran ta yi barazanar rufe mashigin ruwan Hormuz idan ƙasashen na yamma suka ƙaƙaba mata wani sabon takunkumin karya tattalin arziki.
Ƙasashen Tarayyar Turai da kuma Amirka sun zargi Teheran da fakewa da shirin samar da makamashi domin mallakar makamin ƙare dangi. Saboda haka suna neman a ƙaƙaba mata wasu sabbin takunkuman karya tattalin arziki. Sai dai ƙasashe da ke maƙobtaka da Iran ɗin sun nemi a bi hanyoyin dipolomasiya wajen warware rikicin na nukuliyar ƙasar. A baya dai ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi harin sanya takunkumi akan cinikin mai da kuma Bankunan kasar ta Iran.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita:Abdullahi Tanko Bala