Rasha: An kama gomman mutane bayan mutuwar Navalny
February 17, 2024Wata kafar yada labarai ta internet ta kasar ovd.info ta ruwaito cewar a birnin St Petersburg kadai, an kama mutum fiye da 60 sakamakon sanar da mutuwar Navalny da ya yi kaurin suna wajen caccakar lamirin gwamnatin shugaba Putin. Faya-fayan bidiyo da aka wallafa sun kuma nuna yadda jami'an 'yan sandan ke kama wadanda suke aje furanni da kuma kunna kyandira domin nuna alhinin mutuwar Navalny.
A share guda, gwamnatin Birtaniya ta gayyaci jami'an diflomasiyyar Rasha domin tabbatar da cewa sun daura alhakin mutuwar Navalny kan hukumomin Rashaalhakin mutuwar Navalny kan hukumomin Rasha
A birnin Landan, gomman mutane ne dauke da kwalaye suka yi jerin gwano a gaban offishin jakadancin Rasha suna cewa, a dakatar da kisan gillar da Putin ke yi. Kasashen yammacin Turai dai na ci gaba da yin Allah-wadai tare da daura alhakin mutuwar madugun adawan kan shugaba Vladmir Putin.