Rasha bata da sojoji a gabacin Ukraine
April 11, 2014Talla
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya karyata zargin da ake wa Moscow na jibge sojoji a kan iyakarsu da Ukraine ta gabashi, yankin da ke neman ballewa daga Kiev. Ya ce basu da jami'an tsaro a wannan yanki kamar yadda a ke zargi. Lavrov ya ce ko shakka babu akwai 'yan Rasha da ke zama a yankin, kasancewar wuri ne da ke da dumbin jama'a. Gwamnatin rikon kwaryar kasar Ukraine dai ta zargi Moscow da kasancewa ummul aba'isin boren da ke gudana a yankin gabashin kasar da suka hadar da birnin Donetsk da Lugansk, inda masu goyon bayan Rasha ke ci gaba da mamaye gine ginen gwamnati, kuma ke neman a basu 'yancin cin gashin kai.
Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Auwal Balarabe