Ukraine ta shiga damuwa kan atisayen hadin gwiwa
January 16, 2023Rundunar sojin kasashen Rasha da Belarus sun soma wani atisayen soja na hadin gwiwa a wannan Litinin, kuma tuni wannan matakin ya soma haifar da fargaba ga gwamnatin Ukraine da aminanta na kasashen yamma da ke kallon matakin a matsayin wata sabuwar dabara da Mosko ta bullo da ita don ganin ta yi nasara a mamayar Ukraine.
Tun bayan barkewar yakin a Gabashin Turai a watan Febrairun bara, fadar Kremlin ke samun taimakon Belarus inda daga filin kasar take samun damar kai wasu munanan hare-hare kan Ukraine.
A daya bangaren, Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock da ke ziyarar aiki a birnin Hague na kasar Netherland, tana duba yiwuwar ganin an dauki matakin shari'a a gurfanar da Shugaba Vladimir Putin na Rasha a gaban kotun Hukunta manyan laifuka ta Duniya, bisa zargin da ake masa na tafka laifukan yaki a fadan da suke yi da Ukraine.