Rasha da Chaina na zame wa Amirka barazana
October 27, 2022Talla
A yayin da take gabatar da wata taswira mai kunshe da sabbin dubarun tsaro a shekarun masu zuwa, ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagone ta ce Chaina na kasancewa wani gagurimin kalubale mafi muni ga harkokin tsaron cikin gida, duba da wasu take-taken da kasar ke yi a sassa da dama musamman ma barazanarta a yankin Taiwan.
Sai da kuma Pentagone ta ce Rasha ta fi kasance barazana mafi hadari a gareta a yanzu, duba da mamayar da take ci gaba da yi a Ukraine da ma barazanarta na amfani da makaman kare dangi a yakin da take gwabzawa, lamarin da ka iya dagula al'amurra a ciki yanayin da duniya ta fada a yanzu na siyasar duniya mai cike da hayaniya.