Rasha da Indiya na nazarin hadin gwiwar kera makamai
November 8, 2022Talla
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce sun tattauna tare da takwaransa na Indiya a birnin Moscow shirin hadin gwiwa na kera makamai na zamani.
Karo na biyar kenan a cikin wannan shekarar da Lavrov ke tattaunawa da ministan harkokin wajen Indiya Subrahmanyam Jaishankar.
Kasashen biyu na kokarin karfafa dangantakar kasuwanci da kawancen hadin gwiwa ta fannin makamashin nukiliya da kuma tafiya sararin samaniya.
Tsawon shekaru Indiya ta dogara ga Rasha wajen sayen makamai. Haka kuma Rasha ita ce ta hudu wajen sayen magunguna da dangoginsu daga Indiya.