Taron matakan tsaro bayan Amirka ta janye sojinta na Siriya
February 14, 2019Talla
Yayin taron da zai gudana a wannan Alhamis din shugaba Erdogan na Turkiya da takwaransa na Iran Hassan Rouhani za su duba yiwuwar hadin gwiwa a batun mayar da al'ummar kasar ta Siriya da ke zaman gudun hijira a kasashen ketare. A makon da ya gabata ne mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Vershinin ya bayyana cewar Rasha ta shirya tsaf don hana ballewar sabon rikici a Siriya, bayan janye sojojin Amirkan, kasashen Rasha da Iran sun jima suna ba rundunar sojin Siriya hadin kai a fannin tsaro yayin da Turkiyya ke bayan wasu kunyiyoyin 'yan tawayen da ke neman hambarar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.