Rasha da Iran za su ci gaba da yin aiki tare
November 1, 2017Talla
Shugaba Hassan Rouhani a na shi bangaren ya yaba da dangantakar da ke a a tsakaninsu na bunkasar tattalin arziki da kuma yadda suke yaki da ayyukan ta'addanci a yankunansu. A yarjejeniyar da aka kulla da Iran da wasu kasashen duniya shida, Iran ta amince ta takaita shirinta na nukiliya inda a daya bangaren za a janye takunkumin da aka sanya ma ta.
Amirka karkashin mulkin shugaba Donald Trump ta yi barazanar janyewa daga yarjejeniyar don a cewarta Iran ta sabawa dokokin da yarjejeniyar ta gindaya. Kasashen Britaniya da Chaina da Faransa da Jamus da Rasha da kuma kungiyar EU da suka kulla yarjejeniya sun ce za su ci gaba da aiki da ita duk da matakin Amirka na janyewa.