Zargin Rasha da jefa duniya cikin rikici
September 21, 2022Tashe-tashen hankula da matsalolin tsaron suna cikin abin da ake mayar da hankali a taron shugabannin kasashen dunyia na shekara-shekara a zauren Majalisar Dinkin Duniya, inda Shugaba Joe Biden na Amirka ya nuna damuwa kan yakin da Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine. Kuma wannan ya kasance daya daga cikin manyan matsalolin da suka dauki hankali a zauren taron na zama kutsen Rasha a Ukraine, inda Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya bukaci amfani da tataunawa domin samun zaman lafiya tsakanin bangarorin.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya zargi Rasha da karya ka'idojin kasashen duniya na zamani da mayar da duniya surkukin daji da mai karfi zai yi abin da ya ga dama. Sannan Shugaba Macron ya kara da cewa Rasha wadda take da kujerar dindindin a Kwamitin Sulhu, ta dauki matakin kutse kan wata kasa da karya tsaro, ta hanyar hawan kawara ga tanade-tanaden ka'idojin Majalisar Dinkin Duniya na daidaito tsakanin kasashe.
Sannan shugaban na Faransa ya yi watsi da masu cewa kasashen Yammacin Duniya na kokarin kare tsaffin maradun duniya ne, inda ya ce abin da Rasha take yi karkashin jagorancin Shugaba Vladimir Putin na shafan mutane.
Shi ma Shugaba Macky Sall na kasar Senegal wanda yanzu haka yake jagorancin kungiyar kasashen Afirka ya nuna damuwa kan yakin da ke faruwa a Ukraine sakamakon kutsen Rasha, duk da har yanzu galibin kasashe masu tasowa na Afirka suna ci gaba da zama 'yan ba-ruwanmu, wanda ya ce tun bayan zaman Majalisar Dinkin Duniyar da shekarar da ta gabata, duniya ta kara shiga mawuyacin hali.
Shugaba Gabriel Boric na kasar Chile ya bukaci majalisar ta tsaya kan kudurorinta babu nuna son kai bisa wani bangare ko wata kasa a duniya. Sannan ya bukaci ganin ci gaba da samun zaman lafiya na siyasa a kasashen yankin Latin Amirka.
Shugabannin kasashen na duniya na ci gaba da jawabai a taron na shekara-shekara kuma matsalolin tsaro da kutsen da Rasha ta kaddamar kan Ukraine gami da sauyin yanayin na daga cikin manyan abubuwa da suke ci gaba da daukan hankalin shugabannin.