SiyasaTurai
Tashin hankali na ruruwa a tsakanin Rasha da Ukraine
April 1, 2021Talla
Zelenskiy ya zargi Rasha da jibge dakarun soji a kan iyakar Ukraine. Sai dai mai magana da yawun gwamnatin Rasha Damitry Peskov ya musanta wannan zargin.
''Rasha tana tura dakaru ne a cikin kasarta. Bai kamata wani ya nuna damuwa a kan hakan ba. Kasarmu ta Rasha na daukar matakan kare iyakokinmu ne.'' inji Mr. Peskov
Ukraine da Rasha sun fara samun takun-saka a shekara ta 2014 lokacin da Rasha ta mamaye yankin Crimea, kuma ana zargin hukumomin Rasha sun bayar da gudunmawa ga 'yan tawaye a yankin Donbass na Ukraine don tayar da zaune tsaye. Daga baya an kulla yarjejenyiar zaman lafiya amma kuma a baya-bayan nan Ukraine ta yi zargin an kashe mata sojoji guda hudu.