1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar sulhu tsakanin Rasha da Ukrain

Abdullahi Tanko Bala
March 29, 2022

Mashawartan Rasha da Ukraine sun fara wata sabuwar tattaunawar sulhu a birnin Istanbul na kasar Turkiyya bayan da aka gaza cimma madafa a tattaunawar da ta gudana a baya a tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/49AXy
Türkei | Verhandlungen zwischen Russland und der Ukraine in Istanbul
Hoto: Turkish Presidency via AP/picture alliance

A cewar wata sanarwa daga fadar shugaban kasar Turkiyya wakilan kasashen biyu Rasha da Ukraine suna ganawar ce gaba da gaba a karon farko a wannan talatar. Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce za su fara ganawa da kowane bangarorin a kebe kafin su hadu gaba daya su tattauna.Yace suna fatan cimma tsagaita wuta cikin hanzari.

Erdogan ya ce ya tattauna ta wayar tarho da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da kuma shugaban Rasha Vladimir Putin yana mai cewa komai na tafiya cikin nasara. Wakilan Rasha da UKraine sun yi tattaunawa har sau uku a baya a kan iyakar Belarus da kuma wata tattauanawar ta kafar bidiyo sai dai al'amuran sun ci tura.

Kiev na so Rasha ta janye sojojinta tare kuma da ba da tabbacin tsaro yayin da Moscow kuma ke bukatar Ukraine ta janye aniyarta ta zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO ta kuma amince da yankunan yan aware a gabashin Ukraine a matsayin kasashe masu cin gashin kansu sannan ta yarda da yankin tsibirin Crimea da Rasha ta kwace a shekarar 2014 a matsayin yankin kasar Rasha.

Turkiyya dai na da dangantaka da dukkan kasashen biyu.