1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban rikicin Rasha da Ukraine

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 10, 2022

Duk da matakan kakaba takunkumi ga kasar Rasha sakamkon hare-haren da take kai wa makwabciyarta Ukraine, har yanzu Rashan na ci gaba da kai hare-hare kan Kyiv.

https://p.dw.com/p/48J2p
Yakin Ukraine | Irpin I 'Yan Gudun Hijira
Dubban 'yan Ukraine na terewa gudun hijira, sakamkon hare-haren Rasha a KasarHoto: Dimitar Dilkoff/AFP/Getty Images

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce kasarsa za ta koma kan kafafunta da kuma zama mai cikakken iko, idan al'amura suka saisaita. A cewarsa kasashen yamma sun hada karfi waje guda, suna kakabawa Rashan Takunkumi, kuma koda ta kai hari Ukraine ko ba ta kai ba da ma suna da niyyar sa mata Takunkumai kuma babu makawa sai sun saka mata.

Takunkumin kasashen wajen a kan Rasha dai yana matukar shafar tattalin arzikin Moscow, inda tuni darajar kudin kasar ta yi mummunar faduwa yayin da ake fargabar karewar wasau abubuwa a shagunan kasar. Tuni dai dubban 'yan gudun hijira ke kauracewa kasar Ukraine din domin tsira da rayukansu, sakamakon hare-haren da dakarun Rasha ke kaiwa babu kakkautawa. 

An dai gaza cimma matsaya a karo na uku, yayin taron tattaunawa domin shawo kan rikicin tsakanin Rashan da makwabciyarta Ukraine. Taron karo na uku dai, ya gudana a kasar Turkiyya tsakanin mininstan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ciki har da Majalisar Dinkin Duniya, ke nuna bacin ransu kan harin bam da ya yi sanadiyar mutuwar yara uku a asibitin yara da ke birnin Kyiv.