Gobara ta tashi a wasu asibitocin Rasha
May 12, 2020Talla
Hukumomi a kasar Rasha sun dakatar da aiki da na'urar numfashi wato Ventilator a wasu asibitoci guda biyu da ke biranen Mosko da St. Petersburg sakamakon wata gobara a asibitocin da ta hallaka wani majiyyaci guda da kuma ake zargin na'urar ce ta haddasa ta. A asibitocin ne ake jinyar masu dauke da cutar corona a kasar ta Rasha.
Kasashen Rasha da Indiya inda annobar ke kara ruruwa sun matsa kaimi wajen ganin an sassauta dokar kulle a kasashen domin ceto tattalin arzikinsu da ke neman ya durkushe sanadiyyar annobar ta COVID-19.