1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a sansanin soji ya hallaka jami'an tsaro

Binta Aliyu Zurmi
December 26, 2022

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da mutuwar wasu jami'anta 3 bayan da tarkacen wani jirgi mara matuki na kasar Ukraine da suka harbo ya fada musu a wannan Litinin din.

https://p.dw.com/p/4LQVR
Russland Luftwaffenbasis Engels | Tupolew Tu-95
Hoto: Russian Defense Ministry/AP/picture alliance

A cewar ma'aikatar tsaron wannan shi ne karo na biyu da sojojin Ukraine ke amfani da jirgi mara matuki a yunkurin kai hari a sansanin sojoji da ke kudu maso gabashin birnin Moscow a wannan wata.

Wannan yunkurin hari har sau biyu na nuna alamar yadda Rasha ke fuskantar kalubale, duk da cewa Ukraine ba ta fito ta dauki alhakin harin ba, amma sun bayyana cewar ramuwar gayyace a kan mamayar da Rasha ke ci gaba da yi a ka 
sarsu.

Rasha na ci gaba da kaddamar da hare-hare a manya da kananan birane a cikin Ukraine, ko a karshen makon da ya gabata an kai wani mumunan hari a Kherson inda mutum 10 suka rasa rayukansu yayin da wasu 58 suka jikkata sakamakon hari ta sama.