1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin sama ya fadi a Rasha

Abdul-raheem Hassan
October 10, 2021

Ma'aikatar agajin gaggawa ta kasar ta ce akwai tabbacin mutane bakwai sun tsira da rai a cikin mutane 23 da jirgin ya fadi da su yayin da yake tashi.

https://p.dw.com/p/41ULT
Russland | Sibirien | Flugzeug Absturz Symbolbild
Hoto: Alexander Patrin/AA/picture alliance

Hukumomin sun ce jirgin ya fado ne a lokacin da yake kokarin tashi sama, an tabbatar da samun mutane bakwai da rai bayan faduwar jirgin, kuma tuni aka garzaya da su asibiti, sai dai daya daga cikinsu na cikin mawuyacin hali a cewar likitoci.

Hotunan da ma'aikatar agajin gaggawa a kasar Rasha ta wallafa sun nuna yadda jirgin ya rabu gida biyu. A cewar kamfanin dillancin labarai na Interfax, jirgin da ya fadi mallakar wani kamfanin sa kai ne da ke taimakon Sojoji. Wannan dai shi ne hatasrin jirgin sama na biyu da ya faru a kasar Rasha a shekarar 2021.