1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: Iran ta karyata ba wa Yemen makamai

Zainab Mohammed Abubakar
January 31, 2018

Rasha ta yi watsi da shaidar da Amurka da kwararrun MDD suka gabatar, da ke zargin Iran da ba wa mayakan tawayen Houthi na Yemen makamai masu linzami

https://p.dw.com/p/2rsEX
UN-Sicherheitsrat in New York | Thema Chemische Waffen in Syrien | Wassili Nebensja, Russland
Hoto: picture-alliance/Zuma Press

Rashan ta nunar da manufarta na hawa kujerar naki a kudurin neman kakabawa Iran sabbin takunkumi takunkumi.

Jakadan Rasha Vassily Nebenzia ya ce, har yanzu babu tabbaci ko makamai masu linzamin da sauran makamai da 'yan tawayen suka yi amfani da su, a Iran aka kera, ko kuma an yi jigilarsu ne kafin a sanyawa Yemen din takunkumin sayen makamai a shekara ta 2015. Hakan dai na dasa ayar tambaya dangane da sakamakon binciken tawagar kwararrun na MDD.

Nebenzia ya fadawa manema labaru cewar, Iran ta karyata ba wa Yemen makamai. A cewarsa dai, Yemen ta dade da tara makiamai, kasancewar a lokacin gwammatin marigayi Ali Abdullah Saleh, kasashe masu yawa ne suka shiga gasar ba wa Yemen din makamai.