1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani jirgin sojoji na Rasha ya yi batan dabo

Salissou Boukari
September 18, 2018

Wani jirgin saman sojoji na kasar Rasha ya yi batan dabo da cikin daren Litinin wayewar Talata dauke da sojojin kasar guda 14 bisa tekun Bahrum, a daidai lokacin da Isra'ila ke harba makamai zuwa Sirya.

https://p.dw.com/p/353GQ
Syrien Latakia Russischer Kampfjet Sukhoi Su-34
Hoto: picture-alliance/dpa/ V. Savitsky

An daina jin duriyar jirgin ne a lokacin da yake a nisan km 35 da gabar ruwan Siriya, yayin da yake dawowa daga sansanin sojojin sama na Hmeimim na kasar ta Siriya a cewar ma'aikatar tsaron kasar ta Rasha, wadda ta ce jirgin ya bace ne da musalin karfe 11 na dare.

Ma'aikatar tsaron kasar ta Rasha ta kara da cewa, jirgin mai dauke da sojojinta 14 ya bace ne lokacin da wasu jiragen yakin Isra'ila sanfarin F-16 guda hudu suka yi ruwan makamai a yankin Lattakiye da ke zaman yankin da shugaban Siriya Bashar al-Assad ke da farin jini, inda sanarwar ta kara da cewa na'urar da ke a matsyin garkuwa ta kare hare-hare ta kasar ta Siriya ta mayar da martani kan harin na Isra'ila.