1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Blinken na ziyara a kasar Ukraine

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 19, 2022

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg sun bukaci Rasha da ta kawo karshen kutsen da take a kan iyakarta da Ukraine.

https://p.dw.com/p/45jF2
Jamus I Scholz da Stoltenberg a Berlin
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da sakatare janar na NATO Jens StoltenbergHoto: Hannibal Hanschke/REUTERS

Kiran na shugaban gwamnatin ta Jamus Olaf Scholz da sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya biyo bayan fargabar da suke da ita cewa Moscow na shirin mamaye kasar ta Ukraine, inda suka zarge ta da jibge sojojinta kimanin dubu 100 a kan iyakarta da Kiev. Scholz ya nunar da cewa Jamus da NATO na bukatar Rasha ta rage adadin dakarunta da ke kan iyakar tata da Ukraine din, ko kuma su dauki tsauraran matakai a kanta. A hannu guda kuma sakataren harkokin kasashen wajen Amirka Antony Blinken na kan hanyarsa ta zuwa Kiev fadar gwamnatin Ukraine din, a wani sabon yunkurin al'ummomin kasa da kasa na kawo karshen takaddamar da ke tsakanin Ukraine da Rasha. Ana dai sa ran Blinken zai gana da Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine da kuma takwaransa ministan harkokin kasashen waje na Ukraine Dmytro Kuleba a fadar gwamnati ta Kiev. Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Amirkan, ta nunar da cewa makasudin ziyarar ta Blinken shi ne jaddada goyon bayan Washington ga Kiev. Rahotanni sun nunar da cewa Blinken zai zarce Berlin fadar gwamnatin Jamus, domin ganawa da takwararsa ministar harkokin kasashen waje Annalena Baerbock kafin daga bisani a ranar Jumma'a ya gana da ministan harkokin kasashen ketare na Rasha Sergei Lavrov bayan wata tattaunawa da suka yi a Talatar wannan mako ta wayar tarho.