Rasha na fatan warware rikicin Yukren ta hanyar diflomasiya
March 10, 2014Shugaban kasar ta Rasha ya sanar wa Firaminista David Cameron na Birtaniya cewa shi ma yana bukatar a shawo kan rikici ta hanyar tatttaunawa kuma zai yi magana da babban jami'in diflomasiyar kasarsa, Sergueï Lavrov kan batun gungun masu tattaunawa.
Ana sa ran cewa za'a ga alamu na farko tun daga wannan Litinin din (10.03.2014), kan batun gungun masu tatttaunawa kamar yadda kasashen duniya ke bukata.
A wata tatttaunawa da Putin din yayi ta wayar tarho da Firaministan kasar ta Birtaniya David Cameron, da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ya nanata cewa matakin da majalisar yankin na Kirimiya ta dauka na kada kuri'ar amincewa da bin Rashar abu ne da dokokin kasa da kasa suka aminta da shi.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Saleh Umar Saleh