Rasha na gargaɗi kan makomar Ukraine
May 13, 2014Mahukuntan Rasha sun buƙaci ƙasashen yamma da su tattauna da gwamnatin riƙon ƙwaryar Ukraine dangane da yadda tsarin ƙasar zai kasance kafin zaɓen da za a gudanar ranar 25 ga watan Mayu idan Allah ya kai mu. Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, ta ce zaben raba gardamar da 'yan awaren gabashin Ukraine suka gudanar a ƙarshen makon da ya gabata, kamata ya yi a ce, ya zama alamar zurfin rikicin da ke gudana a ƙasar, ga mahukuntan na riƙo da ke birnin Kiev.
Daura da haka, mahukuntan na Moskow sun kuma gargaɗi Ƙungiyar haɗin kan Turai ta EU kan faɗaɗa takunkumin da take barazanar yi wa Rashar, inda ta ce wannan zai janyo koma baya ga yunkurin sassanta rikicin. Ranar laraba ne ake sa ran Ƙungiyar tsaro da hadin kan Turai wato OSCE za ta ƙaddamar da wata tattaunawar da ke da burin buɗe hanyar sulhunta rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa.
Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman