SiyasaAsiya
Rasha na nazari kan gwamnatin Taliban
August 26, 2021Talla
Mai magana da yawun shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ya sanar da cewa za su sanya ido su ga yadda Taliban za su kare rayukan mutanen Afghanistan da jami'an jakadancin Rasha a kasar kafin ta sanar da amincewa da gwamnatin ta Taliban.
Hukumomin na Rasha sun ce suna son ganin zaman lumana ya dawo wa Afghanistan kuma suna fatar za a dakatar da kwararar muggan kwayoyi daga kasar.