1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen yammacin duniya sun yi wa Rasha barazana

Abdourahamane Hassane
January 25, 2022

Shugabanin kasashen yammacin duniya sun yi barazanar kakaba wa Rasha takunkumin karya tattalin arziki mafi muni wanda ba su taba sakawa kasar ba rinsa idan ta kuskura ta kai hari a Ukraine.

https://p.dw.com/p/464Yi
Shugaban Rasha Wladimir Putin
Shugaban Rasha Wladimir PutinHoto: Mikhail Metzel/Sputnik/Kremlin Pool Photo via AP/picture alliance

Firaminitan Birtaniya Boris Johnsonn ya ce yin haka shi ne mafi cancanta: Ya ce ''Kuma Ina tsamanin ya dace a ce mun ga abokanmu na Turai sun kasance a shirye suke su amince da takunkumin da zaran Rashar ta mamaye Ukraine. Kasashen yammancin duniyar, na zargin Rasha da ajiye sojoji sama da dubu dari a kan iyakarta da Ukraine wacce take da nufin mamayewa. Amirka ta saka sojoji sama da dubu takwas cikin shirin ko ta kwana domin agazawa dakarun rundunar tsaro ta NATO da ke jibge a kasashen Romeniya da Bulgeriya.