1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na son tura wa Mali da takin zamani

Abdourazak Maila Ibrahim MAB
October 4, 2022

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putine ya bayyana aniyar samar wa Mali da takin zamani da ya yi karanci a kasar, sakamakon takukuman da kasashen Yamma suka sanya wa Rasha bayan da ta mamaye Ukraine.

https://p.dw.com/p/4HjsI
Russland Mali Abdoulaye Diop  Sergey Lavrov
Hoto: Alexander Shcherbak/dpa/picture alliance

Wata sanarwa da fadar shugaban Rasha Putin ta fitar, taa nunar da cewa ya tattauna da shugaban mulkin sojin kasar Mali ta waya Assimi Goita, inda Putin ya ce a shirye yake ya raba kimanin tonne dubu 300 na takin ga kasashen da ke bukata ciki har da Mali.

Kanal Assimi Goita ya rungumi Rasha hannu bi-biyu bayan da ya raba gari da Faransa, inda baya ga fannin tsaro yake neman kyautata alakar Mali da Rasha a sauran fannonin.