Rasha na tsananta hare-hare a Ukraine
March 23, 2023Talla
Wannan dai wani kakkausar martani ne a daidai lokacin da ake kokarin nemo matakan diflomasiyya da nufin kawo zaman lafiya a yakin na Ukraine da yanzu ya kai watanni 13 na gwabzawa.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy, ya bayyana takaicin yadda hare-haren ke sauka kan gidajen marasa karfi, yana cewa Rasha na bude wuta kan mutane masu rauni irin kananan yara.
Hare-haren dai na fadawa ne a kan rukunan gidaje da ke a kudancin birnin Zaporizhzhia.
A wasu hare-haren kuwa, dakarun Ukraine sun yi nasarar kakkabo jiragen Rasha marasa matuka 16 daga 21 da ta harba a kusa da birnin Rzhyshchiv da ke kudancin kasar.