1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na yi wa 'yan'yanta rigakafin corona

December 5, 2020

Kasar Rasha ta fara allurar rigakafin cutar corona a wannan Asabar, inda ake yi wa wadanda suka fi hadarin kamuwa da cutar. Wannan dai allura ce da ake yin ta a kyauta.

https://p.dw.com/p/3mGap
Russland Moskau | Erste Impfungen gegen das Coronavirus
Hoto: Iliya Pitalev/dpa/Sputnik/picture alliance

A tashin farko dai ana yi wa jami'an lafiya ne da malaman makaranta gami da masu kula da walwalar jama'a rigakafin a sabbin cibiyoyin da aka bude a fadin Mosko babban birnin kasar.

Akalla dai akwai cibiyoyi 70 da aka samar saboda wannan aiki.

Rashar dai na daga cikin kasashen da suka sanar da cewa sun sami nasarar hada allurar rigakafin coronar cikin watan Agusta.

Allurar mai suna Sput-nik V da ba a sanar da lokacin da ake iya yi wa dukkanin 'yan kasar ba, a kyauta za a yi wa al'umar kasar.

Alkaluma na cewa sabbin kamuwa da cutar ta corona a yau Asabar a Rasha, sun kai mutum dubu 28 da 780.