1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta ce dakarunta na janyewa daga kan iyakar Ukraine

May 21, 2014

Tun a ranar Litinin fadar Kremlin ta ce shugaba Vladimir Putin ya ba da umarni da a fara janye dakarun, amma NATO ta ce har yanzu ba wata alamar janyewar.

https://p.dw.com/p/1C4Cw
Ostukraine Krise Checkpoint bei Slowjansk 15.05.2014
Hoto: Vasily Maximov/AFP/Getty Images

Rasha ta ce dakarun da ta girke don yin wani atisayen soji a kusa da kan iyakar Ukraine sun kwance kayayyakinsu kuma sun doshi tashoshin jirgin kasa da filayen jiragen sama don komawa barikokinsu na dindindin da ke cikin Rasha. Sai dai kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta ce ba ta ga wata alamar janyewar sojojin ba. Fadar Kremlin a birnin Mosko ta ce tun a ranar Litinin shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin ya fada wa ministan tsaro da ya ba wa dakarunsa umarnin janyewa daga yankin kan iyaka da Ukraine, wadda ilahirin jihohin ta na gabaci suka koma karkashin ikon 'yan tawaye masu goyon bayan Rasha.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu