1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta ce sojojinta sun mutu a Ukraine

January 2, 2023

Hukumomin kasar Rasha sun sanar da mutuwar mayakan kasar da ke yaki a Ukraine, bayan wani hari da sojojin Ukraine suka kaddamar a kansu a yankin Donetsk.

https://p.dw.com/p/4Lejm
Hoto: RIA Novosti/SNA/IMAGO

Ukraine ta ce ta hallaka daruruwan dakarun Rasha a daren sabuwar shekara, bayan samun taimakon makaman yaki daga Amirka a daidai kuma lokacin da Rasha ke tsananta hare-hare ta sama a kasar.

Rundunar sojin Rasha dai ta ce mayakanta 63 ne suka mutu a wani harin rokoki da sojojin Ukraine suka kai wani ginin da ke dauke da dakarunta a gabashin yankin Donetsk.

Ba kasafai ba ne dai Rasha ke bayar da sanarwar mutuwar dakarunta a fagen yaki ba.

Ukraine ta ce ta kashe sojojin na Rasha akalla 400, bayan kuma ta kakkabo jirage marasa matuka 22 kirar Iran da sojojinta suka yi a 'yan kwanakin nan.

Mayakan gwamnatin Shugaba Vladimir Putin dai sun kaddamar da luguden wuta a yankunan Ukraine masu yawa, ciki har da Kyiv bbabban birnin kasar, inda ta lalata wasu cibiyoyin samar da wutar lantarki a birnin.