1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta ce tana marhabin da sabon ƙudurin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gabatar game da Iran.

December 11, 2006
https://p.dw.com/p/BuYI

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergej Lawrow, ya bayyana gamsuwarsa ga sabon kundin wani ƙuduri da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya gabatar, game da rikicin da ake yi da Iran a kan batun shirye-shiryenta na malllakar tashoshin makamashin nukiliya. Sabon kundin, wanda Birtaniya da Faransa suka tsara na yunƙurin sake janyo Iran ɗin ne zuwa teburin shawarwari, inji Lawrow. Ta hakan dai, wato an yi la’akari ke nan da bukatun da gwamnatinsa ta miƙa wa kwamitin. Da can dai Rasha ta yi watsi da wani ƙudurin da kwamitin sulhun ya gabatar ne, saboda yana ƙunshe da ɗaukan matakan sanya wa Iran ɗin takunkumi. Bisa cewar ministan harkokin wajen Rashan, Sergej Lawrow dai:-

„Soke batun takunkumi a kundin tsarin wannan ƙudurin na da muhimmanci ƙwarai da gaske. Yanzu batun da muke son mu yarje a kansa da Iran ɗin, ya ƙunshi hana ta bai wa, ko kuma sayar wa wasu ƙasashe ko ɓangarori ne, wannan fasahar. Wannan kuma shi ne dai batun da ya fi damun hukumar kula da makamashin nukiliya ta ƙasa da ƙasa, wato IAEA. Babu dai ambaton tashar nukiliyan nan ta Busher a cikin sabon ƙundin Majalisar Ɗinkin Duniyar. Wannan tashar dai tuni Hukumar IAEA ke sa ido a kan ayyukanta. Sabili da haka, wani batun ambatarta a cikin kundin ma bai taso ba.“