1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takin Rasha ya hau hanya zuwa Afirka

November 29, 2022

Buhunan na takin zamanin da yawansu ya kai ton 20,000 na cikin kayayyakin bukata da ake sa ran za a yi jigilarsu zuwa kasashen Afirka dabam-dabam a 'yan watannin masu zuwa.

https://p.dw.com/p/4KFtU
Hoto: Ozan Kose/AFP/Getty Images

Jirgin farko makare da takin zamani na kasar Rasha ya bar kasar Netherlands a Talatar nan zuwa kasar Malawi. Ofishin sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya(MDD) da ya sanar da hakan ya ce wannan na a matsayin wani bangare na yarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine da majalisar ta jagoranci kullawa a tsakanin Rasha da Ukraine. MDD ta ce za a raba takin zamanin a tsakanin kasashen Malawai da Mozambique.