An fara tattaunawa a tsakanin Rasha da Ukraine
February 28, 2022An fara tattaunawa a tsakanin Rasha da Ukraine a wannan Litinin. Mashawarci na musamman ga shugaban kasar Ukraine Mykhailo Podolyak ne ya sanar da haka.
A gefe guda rundunar sojin kasa ta Rasha ta sanar da cewa fararen hula a babban birnin kasar Ukraine, Kyiv, a yanzu nada damar ficewa daga birnin ta wata babbar hanya wace Rashan ta ce ta bude kuma babu wata fargaba ga rayuwar fararen hula. MDD ta ce kawo yanzu 'yan gudun hijira sama da rabin miliyan guda ne suka tsere wa yakin da ke gudana a Ukraine.
Hakan dai na faruwa ne a yayin da babban zauren MDD zai yi zama na musamman a wannan Litinin a game da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine. Ana kuma sa ran Rashan za ta kasance saniyar-ware a wannan zama, kafin daga karshe MDD ta sanar da matsayarta a kan yakin da Rasha ta assasa a kasar Ukraine wace shugabanta Volodymyr Zelenskyy a wannan Litinin ya yi kira ga kungiyar Tarayyar Turai ta EU da ta yi gaggawar sanya ta a cikin mambobinta.