Rasha ta gargadi Amirka a kan Ukraine
September 15, 2022Talla
A hirarta da manema labaru, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta ce, Rasha na da 'yancin kare yankunanta. Washington dai ta aika wa Ukraine makaman rokoki da za a iya harbawa zuwa nisan kilometa 80, amm har yanzu ta ki bayyana shirinta na aikewa da wasu makaman da ka iya ninka wannan tazarar idan an harba.
Sai dai jami'an Amirka sun ce Ukraine ta yi alkawarin cewar, ba za ta yi amfani da makaman rokokin da Washington ta bata wajen kai hari a yankunan Rasha ba. Mahukuntan na Kiev sun nemi agajin makamai kuma sun samu daga Amirka da kasashen Turai, domin abun da suka kira "taimaka musu wajen kariya" daga hare-haren dakarun Rasha.