1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rasha: Gargadin NATO kan jibge makamai a Jamus

Binta Aliyu Zurmi
July 13, 2024

Fadar mulki ta Kremlin da ke Rasha ta yi gargadi cewa muddin Amirka ta jibge makamai masu linzami a kasar Jamus to kuwa manyan biranen kasashen Turai za su fuskanci fushinta a wani mataki na ramuwar gayya.

https://p.dw.com/p/4iG0r
Russland Moskau | Dmitri Peskow und Wladimir Putin
Hoto: Alexei Druginyn/EPA/RIA Novosti/picture alliance

Mai magana da yawun fadar Kremlin Dimitry Peskov ya bayyana cewar suna da karfin makamai da za su dakile duk wani hari na Amirka da kawayenta da zai fito daga makaman da ake shirin kai su Jamus.

Kazalika ya kuma kara da cewar jibge wadannan makamai a Jamus na nufin suna karkashin barazana to kuwa kasashen Turai suma ba za su sha ba.

A ranar Larabar da ta gabata ce dai, a taron kungiyar kwancen tsaro ta NATO Amirka ta bayyana cewar daga shekarar 2026 za ta fara ajiye manyan makamai masu linzami dake cin dogon zango a Jamus, lamarin da ya harzuka Rasha ta kuma sha alwashin daukar fansa.