Rasha ta gurganta shirin agaji zuwa Siriya
July 11, 2023Talla
Kasashe Switzerland da Brazil da Amirka sun yi Allah wadai da matakin da Rasha ta dauka wanda suka danganta da rashin tausayi, suna masu cewa zai jefa miliyon 'yan Siriya ciki hali na tsaka mai wuya a watannin hunturu. Amma a martaninsa, jakadan Rasha Vassili Nebenzia a MDD ya zargi kasashen Yamma da mayar da hannun agogo baya, yana mai cewa tsarin ba ya la'akari da muradun al'ummar Siriya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan hudu a yankin Arewa maso yammacin Syria na bukatar agajin jin ka bayan shekaru da suka shafe suna fama da tashe-tashen hankula da tabarbarewar tattalin arziki da barkewar cututtuka da talauci da kuma iftala'in girgizar kasa a baya-bayannan.