1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta jibge dakaru a iyaka da Ukraine

August 6, 2014

A wata sanarwa da ta fitar a wannan Laraba, kungiyar tsaro ta NATO ta tabbatar da jibge dakaru akalla dubu 20 na Rasha kusa da iyakarta da Ukraine.

https://p.dw.com/p/1Cpf7
Hoto: DW

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta ce Rasha ta jibge dakarunta kusa da iyakar Ukraine, a wani abun da ta kira matakin agaji, ko kwantar da tarzoma. Amma kungiyar ta NATO na ganin cewa wani shiri ne da Rasha ke yi na neman mamaye gabacin kasar ta Ukraine. NATO ta kara da cewa wannan rikici da ke gudana a gabacin kasar, na faruwa ne da hannun Rasha, kuma wannan sabon salo na jibge sojoji kusa da iyakar, wani mataki ne mai hadarin gaske.

A cewar Oana Lungescu, kakakin kungiyar NATO, su dai ba su san abun da ke cikin kan Rasha ba, amma kuma suna iya sa ido kan abubuwan da Rasha take yi a wadannan wurare.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu