1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kaddamar da layin dogo zuwa Kirimiya

Gazali Abdou Tasawa
December 23, 2019

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya kaddamar da sabuwar hanyar jirgin kasa mai tsawon kilomita 19 da ta hada kasar ta Rasha da yankin Kirimiya na kasar Ukraine wanda Rashar ta mamaye a shekara ta 2014.

https://p.dw.com/p/3VHYY
Krim-Brücke Eisenbahnverkehr Eröffnung
Hoto: picture-alliance/dpa/TASS/S. Malgavko

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya kaddamar a wannan Litinin da sabuwar hanyar jirgin kasa mai tsawon kilomita 19, da ta hada kasar ta Rasha da yankin Kirimiya na kasar Ukraine wanda Rashar ta mamaye a shekara ta 2014.

Sai dai tuni Kungiyar Tarayyar Turai ta soki lamirin matakin wanda ta ce ya keta haddin 'yancin kasar Ukraine ne. A wata sanarwa da Josep Borelle mai magana da yawun ministan harkokin wajen kungiyar ta EU ya fitar, ya bayyana wannan hanyar jirgin kasa a matsayin wani mataki na neman cilasta wa yankin na Kirimiya komawa karkashin kasar ta Rasha da kuma nisanta yankin da kasar Ukraine.

 Kungiyar ta EU ta yi kira ga kasar Rasha da ta tabbatar da 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa tsakanin a mashigin ruwan Kertch na yankin na kirimiya zuwa tashoshin jiragen ruwan kasar ta Ukraine na tekun Azov kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.