Rasha ta mamaye Ukraine ta sama da kasa
February 24, 2022Talla
Babban jami'in harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai Joseph Borell ya aike da sammaci ga jakadan Rasha a kungiyar EU Vladimir Chizhov, ya baiyana a hedikwatar tarayyar Turan a Brussels.
Kungiyar ta EU ta yi kakkausar suka tare da yin tir da mamayar Ukraine da Rashar ta yi babu gaira babu dalili a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun EU kan manufofin harkokin waje Peter Stano ya fitar.
Ku ta bukaci Putin ya gaggauta kawo karshen farmakin sannan ya janye sojojinsa da kuma makamai daga yankin Ukraine.
Jamus da EU da kungiyar kawancen tsaro ta NATO duk sun yi Allah wadarai da Rasha kan harin.